Gwamnatin tarayya ta ce daga yanzu matafiya da ke amfani da jirgin sama Najeriya za su riƙa isa filayen jirgin awa ɗaya da rabi kafin lokacin tashin jirginsu.

Ministan kula da harkokin sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika ne ya bayyana haka yau Litinin a shafinsa na twitter.  

A ranar 8 ga watan Yuli ne gwamnatin tarayya ta amince jiragen da ke zirga-zirga a cikin gida su ci gaba da aiki bayan watanni uku da aka shafe ba tare da aiki ba sakamakon bullar annobar korona.

Baya ga matakin isa filin jiragen saman akan lokaci a baya gwamnatin tarayya ta bayyana wasu matakan kariya da ta dauka na dakile yaduwar cutar a tsakanin fasinjojin jiragen sama.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *