Akalla jami’an ‘yan Sanda Bakwai ne suka rasa rayukansu a mumunan hadarin mota da ya faru a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Har yanzu dai ba a san musabbabin abin da ya haifar da Hadarin ba, sai dai shaidun gani da ido sun ce hadarin ya auku ne a Jaji, inda Motar dake dauke da ‘yan sanda ta fadi. 

Wani shaidan gani da ido ya ce ya kirga gawawwakin yan sanda bakwai a tsakiyar titi.

Ya ce baya ga wadanda suka mutu, wasu biyu sun jikkata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *