Jam’iyyar PDP ta ce almundahanar da ta dabaibaye mukarabban shugaban Najeriya Muhammadu  Buhari da APC sune babban abun da ya jefa kasar nan cikin matsanancin talauci da rashin tsaron da ake fuskanta.
Bayan in hakan Ya fito ta ta hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar Kola Ologbondiyan. 
PDP tana kira ga yan Najeriya da kada su karaya su cigaba  da addu’a da bada goyon  ba garemu da yardar ubangiji lokaci ya kusa zuwa.
Jam’iyyar ta ce gwamnatin APC ita ce gwamnatin da tafi kowacce cin hanci a kasar nan. 
PDP ta ce hana binciken wasu daga cikin mukarraban gwamnatin da ake kokarin yi akan tsohon shugaban riko na hukumar  yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ya tabbatar da sa hannun mukarraban APC da makusantanta shugaban kas La cikin zargin.
Jam’iyyar ta ce wannan abun ya kara fito da yanda mukarraban shugaban ke wasoso da dukiyar kasa. 
A cewar jam’iyyar wannan ya kara nunawa karara yanda shuwagabannin APC,  a cikin shekaru biyar da gabata, suka wawashe sama da tiriliyan 14,  daga ma’aikatun gwamnati. 
Ya ce wannan ya nuna dalilin da yasa har yanzu ba’ayi bayani ba akan kudin da aka sata a ma’aikatar tattara kudaden shiga  ta FIRS,  da ma’aikatar bada agajin lafiya NHIS da ma’aikatar bada agajin gaggawa NEMA da kuma ma’aikatar dake kula da ci gaban yankin Niger Delta NDDC da sauran wasu hukumomi da dama. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *