Shahararriyar ‘yar fim din kasar Indiya Aishwarya Bachchan da ‘yarta sun kamu da cutar korona.

Wannan na zuwa ne bayan mijinta Abhishek ya kamu da cutar.

Ministan lafiya na kasar Rajesh Tope ne ya wallafa hakan a shafinsa na twitter.

Ya ce Aishwarya da ‘yarta sun kamu da wannan cuta ne kwana guda bayan shahararren dan wasan kwaikwayon kasar Amita ya kamu.

Sai dai ba a bayyana halin da ita da’ yar ta suke ciki ba kawo yanzu.

Hukumomin kasar sun tabbatar da cewa masu dauke da cutar sun haura dubu dari 8 sannan sama da mutane 28,000 ne suka sake kamuwa a cikin awa 24.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *