Rundunar sojin Najeriya ta lalata sansanin kungiyar Boko Haram bangaren ISWAP.

Rundunar sojin ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce jami’an sojin sun kai harin ne sakamakon bayanan sirri da ta samu kan maboyar ‘yan ta’ addan a Zamfara.

Ta ce sakamakon wasu bayanan sirri da ta samu wadanda suka tabbatar da samuwar wadannan mayaka ya sanya ta kai wannan hari ta sama a ranar 10 ga watan Yuli.

Dakarun rundunar Operation Hadarin Daji ne suka kai simamen cikin dajin Kuyambana da ke kudu maso yammacin jihar ta Zamfara.

Sanarwar ta kara da cewa bayan tarwatsa sansanin wasu da dama daga cikin mayakan sun nemi tserewa a kan ababen hawa, wadanda suma aka bisu aka kashe su daga baya.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana takamaimai mutane nawa aka kashe ba ko kuma nawa aka kama ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *