Gwamnan jihar Gombe Inuwa Ibrahim ya ƙaddamar da dashen bishiyoyi a yankin Wajari da ke ƙaramar hukumar Yalmatu-Deba.

Gwamnan ya ce ana shuka bishiyoyin ne domin magance matsalar zaizayar kasa a jihar.

Ya ce dashen bishiyoyin wanda shine karo na biyu zai taimaka wajen daƙile kwararowar hamada da inganta ƙasar noman.

Ibrahim ya ce gwamnatin jihar na da kudurin shuka bishiyoyi miliyan ɗaya da dubu dari biyu a wannan shekarar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta fara dasa bishiyoyin a makarantu da asibitoci da tituna da ma’aikatu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *