Wasu rahotanni sun bayyana cewa sojojin Najeriya 380 na shirin aje aiki nan da watanni 6 masu zuwa.

Rahotannin sun ce wasu daga cikin jami’an sojin na sahun gaba cikin wadanda sahun gaba a yaki da kungiyar ‘yan ta’ addan Boko Haram.

Majiyar ta ce banda 356 da zasu ajiye aikin sojin, 24 daga cikin su za suyi ritaya ne domin karbar Sarautar Gargajiya a garuruwan su.

Sanarwar ta ce tuni shugaban rundunar sojin Yusuf Tukur Buratai ya amince da bukatar jami’an sojin.

A wani labari na daban Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawal ya ce a shirye suke su amince da kasafin kudi na musamman daga bangaren zartarwa da zai bada damar kara yawan sojojin da kuma saya musu kayan aikin da suke bukata lokacin da suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *