Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ya zama wajibi shugaban tsohon shugaban riko na hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ya amsa zargin da ake masa akan zargin almundahana da cin amanar kasa da ake masa.

Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin sakataren yada labarai na jam’iyyar Kola Ologbondiyan.

Jam’iyyar ta ce Magu bashi da nagartar da ta dace ya rike hukumar EFCC.

Ta ce zaman Magu shugaban hukumar Ya haifar da koma baya a yaki da ake da cin hanci da rashawa.

PDP ta ce ya zama dole ya amsa tambayoyi a gaban bainar jama’a wanda shine jama’a za su amince akan za’ayi gaskiya a binciken.

Jam’iyyar ta ce akwai zargin karya dokoki , inda wasu makusan tansa suke yada labarai ba tare da sa hannun lauya, wanda ba haka ya kamata ba kamata yayi ace shugaban EFCC an kaisa kotu.

PDP ta ce Magu ya zubar da darajar hukumar dake yaki da cin hanci inda yake zabar wanda zai bincika , inda babu wani jami’in wannan gwabnatin, musamman wanda ta bayyana a fili barayin amma har yanzu EFCC bata kamasu ba.

Jam’iyyar ta kuma bukaci a tabbatar an bar alakalai sun binciki wannan zargin da ake wa shugaban EFCC.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *