An kafa hukumar yaki da al’mundahana da yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ne a shekarar 2003 karkashin mulkin tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da zummar gyara wa ‘yan Najeriya zama game da cin hanci da rashawa da ke hana kasar motsi ta fannin ci gaban al’umma.

Daga kafa hukumar ta yakar rashawar ya zuwa yanzu, an sami shugabannin da suka jagorance ta kama daga kan Nuhu Ribadu, Farida Waziri, Ibrahim Lamorde, Ibrahim Magu da kuma sabon shugaban rikon yanzu Mohammed Umar Abba.

Cin hanci da rashawa ne babbar cutar da ke damun Najeriya da ta harde kowa tare da karade lungu da sakon kasar. Ta inda tun daga kan masu mulki har wadanda ake mulka ba wanda ke jin kidan wani saboda kowa dama yake nema ya buga irin tasa gangar.

Yaki da al’mundahana ba karamin kalubale ba ne a kasar da ko masinja da akawun da suke aiki a ofisoshi ba a barsu a baya ba, da kun hadu to suna neman na goro ne kafin ka sami shiga har ka aiwatar da abin da ya kaika ma’aikatar.

Kai hatta ‘yan dako a kasuwa idan ka sake to kuwa za ka sha mamakin yadda zai ha’ince ka, ya kuma bace maka da gani ba tare da abin ya hana shi barci ba. 

Su kuma masu mulkin siyasa ko na soja, suma ba sa kakkautawa wajen gani sun wawuri rabonsu daga dimbin arzikin da Allah ya yi wa Najeriya musamman idan aka yi la’akari da dimbin gangunan man fetur din da ta ke hakowa a ko wace rana.

Tun daga bada ‘yancin kai a Najeriya a shekarar 1960 daga hannun Birtaniya zuwa yanzu, zai yi wuya wani mahalukin ya san yawan adadin dukiyar kasa da jama’a suka wawure kai tsaye ko kuma suka sace a kaikaice zaune a cikin ofisoshin gwamnati da sunan ana aiki.

Da yawan ‘yan Najeriya sun san cewa wutar lantarki da ruwan famfo kadai sun isa matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar. Ballantana kuma a je maganar harkar lafiya da ilimi da fannin sufuri da makamantan abubuwan da ya kamata gwamnati ta samar na more rayuwa.

Hukumar EFCC (Economic and Financial Crime Commission) kamar yadda ake kiranta a turance ko a takaice, ta shiga fafutukar yaki da cin hanci ne da zummar kawo karshen daka wawar da wasu suke wa kudin kasa.

Wanda kuma dole ba za a rasa nasarorin da ta samu ba ko kuma akasin haka. Shugabannin da suka rike ta kowa da irin salon gudanarwar da kuma irin nasarar da kowa ya samu. 

Duk da yake dai a karshe dutse hannun riga ake rabuwa da shugabannin hukumar. Hakan yana matukar jefa shakku ga zukatan ‘yan Najeriya na cewa shin ko dai kullum mai dokar barci ne ne ke buga gyangyadi a yaki da rashawar? Kadan daga nasarorin da efcc ta samu sun hada da cafkewa ko tatso kudaden baitil-malin da aka wawure. 

Malam Nuhu Ribadu wanda dan sanda ne, shine shugaban hukumar na farko tun daga shekarar 2003 da aka kafa ta, kuma an sami nasarori karkashinsa, ciki har da ta kama wa da gurfanar da wasu mutane irin su Marigayi tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha a shekarar 2005. 

Nuhu Ribadu

Sai kuma a 2006 hukumar ta sa sunayen wasu gwamnoni guda 31 daga gwamnoni 36 na Najeriya bisa binciken zargin cin hanci da rashawa. 

Cikin shekarar 2007 ne kuma hukumar ta dakile al’mundahana ta binciki badakalar kamfanin ‘yan kasuwar nan naVaswani Brothers da aka ce sun yi batan dabo kan wani aikin da aka basu a Najeriya, amma daga baya an wanke su bayan an rasa wata hujja tare da kyale su su ci gaba da harkokinsu a Najeriya bayan da an wartake su.

A 2008 ma efcc ta binciki Iyabo Obasanjo-Bello, ‘yar tsohon shugaban Najeriya Obasanjo bisa zargin karbar rashawar naira miliyan 10 daga cikin kudade naira miliyan 30 da aka sace bayan samun rarar kasafin kudin ma’aikatar lafiyar Najeriya.

Kwatsam ana cikin yaki da cin hanci a karkashin Nuhu Ribadu, sai kawai aka ji takaddama ta barke akan shugabancinsa, sannan aka dinga kunbiya-kunbiyar cewa an tura shi kwas. Karshe dai sai aka ga an rantsar da Malama Farida Mzamber Waziri a shekarar 2008 a matsayin sabuwar shugabar hukumar ta efcc.

Farida Waziri

Amma abin da ya daurewa jama’a kai shine, bayan kai ruwa rana akan shugaban efcc na farko Nuhu Ribadu, sai ma da aka rage masa mukaminsa na dan sanda daga matsayin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda zuwa Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, kafin daga bisani aka hankada keyarsa zuwa waje daga hukumar.

Ita kuma Farida Waziri tana cikin jan zarenta ana ta yaba wa sai kawai tsohon shugaban Najeriya Jonathan Goodluck ya hankade ta daga kan kujerarta a shekarar 2010, tare da maye gurbinta da Ibrahim Lamorde a matsayin shugaban rikon kwarya sannan daga baya a ka tabbatar masa da kujerar a matsayin shugaba ba na riko ba.

Ibrahim Lamorde

Lamorde yana rike da hukumar har lokacin da Muhammadu Buhari ya zama zababben shugaban Najeriya a 2015, inda kwanan kujerar shi Ibrahim din ta mulkin efcc ya kare aka kuma nada Ibrahim Magu a matsayin shugaban riko, tare da mika sunansa ga ‘yan majalisar dattawa don tantance shi a matsayin shugaban hukumar.

Ibrahim Magu

To amma kemadagas Sanatocin Najeriya suka ki tabbatar da Magu a matsayin shugaban hukumar, amma dai nan aka barshi a matsayin na rikon kwarya har zuwa lokacin da ajalin kujerarsa ya zo a tsakiyar shekarar nan ta 2020 da rahotanni suka cika duniya kan cewa an cafke Ibrahim Magu, duk da yake hukumar tace gayyatarsa aka yi.

Da farko an yi ta nuku-nukun inda Magu yake, amma ba tabbas. Sai da surutu yayi yawa tare da shaci fadi ne, sai kawai sanarwa ta bayyana daga Shugaba Buhari ranar 10 ga Yulin 2020 da ke tabbatar da dakatar da Magu da kuma nada wani dan sandan da dama a hukumar yake aiki da cewa shine ya maye gurbin tsohon shugaban a matsayin riko.

Sanarwar kuma ta fito ne ta hannun ofishin ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami, sannan a sanarwar an nuna cewa Mohammed Umar zai ci gaba da riko har sai an ga abin da bincike zai haifar na kwamitin da aka kafa su binciki zarge-zargen da ake wa Ibrahim Magu.

Bisa rade-radin da jama’a ke yi shine, wannan magu-magun na dauki dora da sauke wa na shugabnancin hukumar yaki da rashawa, yana taba darajar hukumar da bada rashin tabbas. 

Kasancewar, duk shugaban da aka nada karshe shima sai a ga ana zarginga da banga-banga da wasu masu gida rana ko kuma zargin cewa shugaban ya zama ko kuma ya ki zama dan amshin shatar gwamnati mai mulki. 

Sannan kuma akwai zargin cewa ma ai yawanci shugabannin ana nada su ne don zama karnukan farautar ‘yan adawa da gwamnati a siyasance, inda ake ragargazar su ba tare da tabo shafaffu da mai ba ko da kuwa sun tafka kuruciyar bera, matukar suna dasawa da jam’iyya mai mulkin kasar.

Daga cikin zargin da ake yi, har da yadda Sanatoci da masu rike da madafan iko ke yi wa shugabannin EFCC dirar mikiya da tabbatar da ganin bayansu, musamman idan suka lura cewa, za su fada komar binciken cin hanci da rashawa, tunda satar dukiyar kasa ta zama ruwan dare a Najeriya

Abin jira a gani yanzu shine, shin Muhammadu Buhari zai yi garambawul ga hukumar ta hanyar dasa ta a turbar da za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da nuna sani ko sabo ba.

Daga sashen rahotannin musamman na Radiyon Talaka

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *