Shugaba Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sanya hannu kan kwaskwarimar kasafin kudin 2020 da ya aika majalisar dokokin tarayya.

A jiya ne mai ba shugaban shawara kan harkokin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa shugaban zai sa hannun a shafinsa na twitter.

Kwanaki 29 da suka gabata, Majalisar wakilai ta amince da kwaskwarimar kasafin kudin inda ta kara shi daga N10.5 tiriliyan zuwa N10.8 tiriliyan.

‘Yan majalisar sun kara da naira biliyan hudu na walwalar kungiyar likitoci masu neman kwarewa bayan barazanar yajin aiki da suka yi. 

Hakazalika, majalisar ta amincewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aro kudi har dala biliyan 5.513 don amfanin kasar nan.

Gwamnatin Najeriya ta sanya takunkumi kan daukan aikin yi a ma’aikatun gwamnatin gaba daya. 

Ministar kudi kasafi da tsare-tsare, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana hakan ne yayinda take hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba.

Ta ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da biyan ma’aikata albashi kuma ba za ta sallami ma’aikata ba amma ba za’a sake daukan sabbin ma’aikata. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *