Dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa Ibrahim Magu, ya bukaci shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu Ya bada belinsa.

Magu ya bukaci hakan ne ta hannun lauyansa, a wata wasika da aka rubuta a yau Juma’a 10 ga watan Yuli.

An tsare shugaban hukumar ne bayan da kwamitin da shugaban kasa ya kafa suka gayyace shi a ranar Litinin din da ta gabata.

Ana binciken Ibrahim Magu ne kan zargin almundahana a tsawon lokacin da ya kwashe yana mulkin hukumar.

A labarin da ya gabata, mun kawo muku rahoton inda Magu ya karyata ba mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo kudi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *