Dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Ibrahim Magu, ya ce bai ce ya ba mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo naira biliyan 4 ba.

Magu ya karyata labarin ne yayin da ya gurfana gaban kwamitin bincike da fadar shugaban kasa ta kafa.

Ya ce ko kadan bai fadawa kwamitin ya ba mataimakin shugaban kasa kudi ba.

Ya ce ko shi bashi da kudaden da suka kai haka balle Ya baiwa wani.

Magu ya ce ko kadan ba’a ambaci sunan mataimakin shugaban kasa a tattaunawar kwamitin binciken ba.

Ya kara da cewa bashi da iko kan irin wadannan kudaden, kuma bai bada umurnin ba mataimakin shugaban kasa kudi ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *