Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce bai kamata gwamnatin Najeriya ta hana yin jarrabawar kammala makaranta sakandare ta WAEC.

Atiku ya bayyana hakan ne a a shafinsa na Twitter.

Tsohon mataimakin shugaban ya ce akwai hanyoyin da gwamnatin za ta iya bi wajen gudanar da jarrabawar ba wai ta dakatar da ita baki ɗaya ba.

Ya ce za a iya amfani da manyan ɗakunan taro a makarantun firamare da filayen wasanni da sauran wajen zana jarabawar.

Atiku ya kara da cewa sauran ƙasashen Afrika sun bar Najeriya a baya a fannin ilimi, a cewarsa dakatar da jarrabawar zai iya jawo rikici a ɓangaren ilimi.

Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnatin Najeriya ba ta bari an gudanar da jarrabawar ba, dubban mutane za su tafi kasashe makwabta domin zanawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *