Kungiyar yarbawa ta Afenifere tayi Allah wadai da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana bude makarantu.

Kungiyar ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta koran ministan kan zargin kawo tsaiko ga zangon karatu na shekara guda.

Sakataren kungiyar, Basharun Sehinde Arogbofa ya ce Ya zama wajibi gwamnati ta ba dalibai damar komawa makarantu domin ci gaba da karatu.

Ya ce ministan ilimi Adamu Adamu ya cancanci a kora daga sakamakon daukar wannan mataki.

Gwamnatin tarayya ta kwashe kusan watanni shida tana shirye-shiryen komawa zagon karatun ba tare da cimma matsaya ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *