Babban hafsin sojin sama na Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce rundunarsa za ta ci gaba da matsa kaimi a yaki da ayyukan ta’addanci har ‘yan kasa sun koma gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum kamar yadda suka saba a baya.

Abubakar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar wani rukunin sabbin gidajen jami’an sojin a shelkwatar da rundunar ta kafa a Birnin Gwari dake jihar Kaduna.

Ya ce wannan na daga cikin nauyin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya daura mata, da kuma kudurorin da take dasu na tabbatar da zaman lafiya da walwala.

Abubakar ya kuma yabawa rundunar sojin dake aikin tabbatar da tsaro a Birnin Gwari, bisa namijin kokari da suka yi wajen takaita ayyukan ta’addanci.

Sannan ya bada tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da samar da kayayyakin aiki na zamani da za su taimaka wajen ba jami’an tsaron kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.

Ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa irin goyon bayan da yake ba rundunar sojin sama wajen ganin ta sauke nauyin dake kanta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *