Cibiyar da ke tafiyar da Muryar Amurka ta ce ba za ta sake sabunta bizar daruruwar ‘yan jarida ‘yan kasashen waje da ke mata aiki ba.
Hoto: Radiyon Talaka

Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu sun bayyana wa wasu kafofin labarai cewa, wannan mataki ya fito ne daga sabon jagoransu Micheal Pack da Shugaba Donald Trump ya nada tun shekaru biyu da suka wuce, amma bai sami amincewar ‘yan majalisar kasar ba sai a makwanni kadan da suka gabata, inda ya fara aiki a watan jiya na Yuni.

Idan ba a manta ba daga zuwansa har ya kori shugabannin wasu bangarorin yada labaran gidan a makon farko da ya fara aiki, inda ita kuma tsohuwar shugabar Muryar Amurka Amanda Bennett ta shuri takalmanta suka yi gaba ita da mataimakiyarta ‘yan kwanaki kafin gogan ya shiga ofishinsa na aiki.

Hakika ana ganin Amanda ta yi wa kanta kiyamul-laili don da tuni Pack ingiza keyarta waje, musamman in aka yi la’akari da yadda masu kallon cewa ta tafka ragabza a yanayin shugabancin Muryar Amurka wajen kasa dakile yada manufofin ‘yan gurguzun kasar Sin da makamantansu masu adawa da Amurka.

Micheal Pack ya ce ba zai amince da sabunta visar ma’aikatan jaridar gidan ba, wanda hakan na nufi sai dai su nade kayan su da dan guzurinsu su koma inda suka fito. Pack dai ya sha nanata cewa, duk abin nan da ya ke yi yana cikin yunkuri garambawul ne ga cibiyar aka kafa don kare martabar Amurka.

Sama da shekara 75, yana daga cikin al’adar hukumar gudanarwar Muryar Amurka dauko ‘yan jaridu daga kasashen waje domin yin aiki ga sashen harsuna daban-daban sama da guda arba’in da suke yada shirye-shiye da su zuwa ga kunnuwan miliyoyin mutane a duniya.

Hoto: Radiyon Talaka

Yadda abin yake shine, idan dan jarida daga wata kasa yaga sanarwar daukar aiki a wani sashen harsuna kamar misali sashin Hausa ko Larabci ko Sifaniya ko kuma harshen Sinawa na Mandarin sai ka nemi aikin idan kana bukata ta hanyar cike-ciken takardun neman daukar aikin da ka ci karo da ita.

Idan aka gama duk gwajin da za a yi maka a kan aikin jarida da kuma kwarewarka akan wannan harshen, sai kuma hukumar ta aiwatar da binciken halayyarka tare da aika maka da takardun daukar aiki idan sun gamsu da binciken da suka yi a kanka na zahiri da kuma a asirce.

Wannan takardun na daukar aiki ne zasu baka damar zuwa neman wata bizar da ake kira da suna J1 da zata baka damar shiga Amurka a matsayin wani kwararre a wani fannin dalibta ko koyarwa ko kuma fagen da ba kowa ya kware a kai ba don bada gudunmawar aiki a bangaren. 

Duk da yake dai dama wasu na zargin cewa  akwai ha’inci a yanayin amfani da wannan rukunin bizar da a ka fito da ita don yin musayar dalibai da kwararrun da za su yi karatu da aikin wucin gadi kama daga makwanni zuwa wasu shekaru, amma ba don daukar ma’aikata da za su zauna aikin din-din-din a kasar ba.

Shi yasa ma a tsarin wannan bizar a turance suke ce mata ‘The Exchange Visitor Visa’ wato ‘Bizar Musanyar Maziyarta’ don karatu da ayyukan wucin-gadi. To amma sai a ke zargin wasu ma’aikatun da cewa suna amfani da wannan bizar wajen shigo da ma’aikatan ‘yan share wuri zauna.

Ta inda ake zaton ana rikidar da takardun aikin wucin gadin na J1 zuwa  ma’aikata mazaunan Amurka masu rike da katin shaidar zaman kasar ko ‘green card’ kamar yadda aka fi sani a turance. 

Abin da ba a sani ba shine, shin rashin sabunta bizar ma’aikatan zai iya zama wata dama gare su ta samun takardun zaman kasa na ‘green card’ ko kuwa shi kenan sai dai su yi ciranin saniya ta hanyar tsira da na cikin su zuwa gida.

Lamarin da masana ke ji wa ‘yan jaridar tsoro, musamman yadda ‘yan jaridar suka mike kafa suna ta cin karensu ba babbaka, wajen yada labarai iri-iri masu dadi da mararsa dadi masu bata wa kasashen da suka fito rai, amma ba su damu ba saboda suna fake a Amurka.

Wasu ‘yan jaridar ma idan suka shigo sai su shafe shekaru ba su ziyarci kasashensu ba saboda gudun gamuwa da ramuwar gayya daga gwamnatoci ko masu tsattsauran ra’ayi. To abin fargabar shine in har suka koma kasashensu to komai zai iya faruwa da su don ungulu ta koma gidanta na tsamiya.

Trump dai da tawagarsa a fadar ‘White House’ sun sha sukar Muryar Amurka da cewa kamar lafiyayyen kifi ne amma da rubabben kai. Inda su kuma wasu Amurkawa ke kallon cewa ana musu barnar kudin harajinsu wajen daukar nauyin kafar labaran da suke ganin tuni dalilan kafata ya wuce na yada manufar kasar a idon duniya.

Abin jira a gani shine, shin Trump da mukarrabansa zau sake cin zaben wa’adin mulki karo na biyu ko kuwa abokin hamayyarsa Joe Biden zai rangada su da kasa? Wanda nasarar Biden ce kadai wasu ke ganin za ta iya barin Muryar Amurka da sauran shan ruwa.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Hakika wannan rediyo zai iya Zama zakaran gwajin dafi a dan kankanin lokaci mai zuwa ganin yanda yake fitar da labarai da dumi dumin su kuma sahihai.
    .
    Allah ya Kara daukaka