Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya ce rashin samun wadataccen wutar lantarki na durkusar da masana’antu da harkokin ci gaba a Najeriya.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a lokacin zaman jin ba’asi daga Kwamitin majalisar dake kula da harkokin wutar lantarki karkashin jagorancin shugaban masu rijaye na majalisar Alhassan Ado Doguwa.

A cewarsa majalisar za ta yi dukkanin mai yiwuwa tare da fito da sabbin tsare-tsare da bin diddigi dan tabbatar da cewa wutar lantarki ya inganta a fadin Najeriya.

Gbajabiamila ya ce sanin kowa ne duk da makudan kudade da ake zubawa a bangaren wutar har yanzu ba za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu ba.

Sannan ya yabawa kwamitin majalisar wanda a cewarsa tun bayan kafa shi bai zauna ba, domin tabbatar da komai na tafiya yadda ya kamata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *