Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta kaddamar da kwamiti na musamman domin shirin ko ta kwana na kubutar da rayuka da dukiyoyin al’umma daga ambaliyar ruwa.

Shugaban hukumar Muhammadu Muhammad, ya bayyana haka a lokacin da yake rantsar da kwamitin a Abuja.

A cewarsa a koda yaushe hukumar na zaune a cikin shiri musamman ma idan aka yi hasashen samun ambaliyar a lokacin damina, domin ganin ba ta yi barna sosai ba.

A ranar 21 ga watan Janairun wannan shekarar ne hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya NiMet ta fitar da rahoto kan hanyoyin da za a bi wajen takaita faruwar ambaliyar.

Muhammad wanda ya samu wakilcin shugaban sashen kula da bincike da tsare-tsare Kayode Fagbemi ya wakilta, ya ce akwai sabbin dabaru da hukumar ta fito da su da za su takaita barnar da iftila’in ya saba yi a baya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *