Runduna ta musamman da gwamnatin tarayya ta kafa domin hana fasa kwabri a kan iyakokin kasa ta kama wata mota da aka boye buhunan shinkafa masu nauyin kilogram 50 guda 140 a cikin yashi.

Rundunar dake aiki a jihohin Arewa ta tsakiya da ya hada da jihohin Niger, Kwara, Kogi da Benue sun kama motar ce a Kontagora dake jihar Niger.

Shugaban rundunar dake da shelkwata a Ilorin na jihar Kwara, Muhammad Garba, ya ce shinkafar da rundunar ta kama ya kai na  naira milliyan 2 da dubu dari da 42.

Ya ce a cikin kwanaki 40 da suka gabata, rundunar ta kama mutane 53 da ake zargi da fasakwabrin kayayyaki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *