Babatunde Fashola
Ministan Ayyuka

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kashe naira biliyan dari da 9 da milliyan dari da 87 wajen gyaran hanyoyi da kuma dakunan kwanan dalibai a jihohi 4 dake Najeriya.

Ministan ayyuka da samar da gidaje Babatunde Fashola, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya ce ma’aikatarsa ta gabatar da wasu takaddun yarjejeniyar aikace-aikace ga majalisar.

A nasa jawabin ministan ilimi Adamu Adamu, ya ce majalisar ta amince da yarjejeniya tsakanin kwalejin kimiyya da fasaha na Kaduna, da kuma masu zuba jari domin gyaran dakunan kwanan dalibai.

Ya ce kwangilar da za a kashe sama da naira milliyan dari 7 da 44 zai kammala ne a cikin shekaru 15 masu zuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *