ABDULLAHI UMAR GANDUJE
GWAMNAN KANO

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nadin Abdurrazak Salihi a matsayin shugaban hukumar tara kudaden shiga ta jihar.

Mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Abba Anwar ya tabbatar da haka ga manema labarai a Kano.

Anwar ya ce nadin sabon shugaban hukumar zai fara aiki ne nan take, gwamnan kuma ya godewa tsohon shugaban hukuma Bala Muhammad bisa jajircewa da ya yi wajen ci gaban hukumar.

Sannan ya bukaci sabon shugaban hukumar da ya yi aiki da kishi da kuma sauran ma’aikatan hukumar domin tabbatar da ci gaban jihar.

Kafin nadin nasa Salihi shine shugaban hukumar tattara bayanan yadda ake gudanar da harkokin kudi na jihar, sannan ya yi aiki a bangarori daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *