Paul Onuachu

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Paul Onuachu, ya kamu da cutar korona.

Dan wasan ya kamu da cutar ne a daidai lokacin da sakamakon gwajin da aka yiwa abokan wasansa Stephen Odey da Cyril Dessers ba kungiyar kwallon kafa ta Jamus Genk ya nuna basu dauke da cutar.

Dan wasan mai shekaru 26 ya baro kasar Belgium ne tare da abokan wasansa na gida Victor Osimhen da Imoh Ezekiel a ranar 27 ga watan Mayu.

Onuachu ya koma kungiyar da yake yiwa wasa ne ranar 28 ga watan Yuni bayan ya makale a Legas, sakamakon hana zirga-zirgar jiragen sama domin dakile yaduwar cutar.

Dan wasan dai shine na 2 a cikin ‘yan wasan Super Eagles da suka kamu da cutar bayan Akpan Udoh da ya kamu a watan Fabrairun wannan shekarar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *