Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce cutar korona ta sake kama mutane 460 bayan gwaje-gwaje da aka gudanar a ranar Laraban da ta gabata.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da take fitarwa kullum a shafinta na twitter.

NCDC ta ce mutane 265 sun warke daga korona sannan an sallame su daga cibiyoyin killace masu dauke da cutar da ke faɗin Najeriya a ranar Laraba.

Hukumar ta kara da cewa mutane 15 ne suka rasa rayukansu a cikin sa’o’i 24 a faɗin Najeriya.

A Lagos, jihar da annobar ta fi tsanani tun bayan ɓullarta Najeriya, an sake gano masu korona 150.

An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani dan kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Hukumar ta NCDC ta ce ta rubanya yawan gwaje-gwajen da take gudanarwa a kullum, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji fiye da dubu ɗaya cikin sa’a 24.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *