Hukumar kula da ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen ketare ta ce akalla ‘yan Najeriya da suka makale a hadaddiyar daular larabawa Dubai 246 ne suka iso gida sakamakon.

Hukumar wacce ta sanar da dawowar mutanen ta shafin ta na twitter ta ce mutanen sun sauka ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas.

Ta ce gwaji ya nuna cewa dukkanin wadanda aka dauko a tafiyar basu dauke da cutar korona, kuma za su killace kawunansu na tsawon makwanni 2 masu zuwa inda za a sake musu gwajin.  

Tun bayan bullar cutar korona a kasashen duniya, gwamnatin tarayya ta fara jigilar ‘yan Najeriya dake kasashen ketare da suke da kudurin dawowa gida.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *