Fadar shugaban kasa ta maye gurbin dakataccen shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da Muhammad Umar.

Muhammad shine babban daraktan gudanarwa na hukumar ta EFCC, kuma shine zai kasance mukaddashin shugaban hukumar kamin daga bisani a nada Wanda zai jagoranci hukumar.

Ibrahim Magu ya shafe shekaru 5 yana jagorancin hukumar a matsayin shugaban riko shugaban hukumar.

Sai dai a ‘yan kwanakin nan an zarge shi da almundahanar wasu makudan kudade.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *