Majalisar dattawa Najeriya ta sauya dokar wanda ya cancanci rike mukamin shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya zuwa shekaru hudu, bayan ta yi nazari a kan tsohuwar dokar ‘yan sanda ta shekara ta 2004 da kuma sauya ta zuwa ta 2020.

Da ya ke gabatar da rahoto a kan kudurin shugaban kwamitin kula da harkokin ‘yan sanda na majalisar Halliru Jika, ya ce mafi yawan masu ruwa da tsaki ba su goyi bayan yadda majalisar ke tabbatar da shugaban ‘yan sanda yayin wani taron jin ra’ayoyin jama’a.

Ya ce an samu rabuwar kawuna a kan wannan doka da ta bukaci tabbatar da nadi ko cire shugaban ‘yan sanda da majalisa ke yi.

Dangane da naɗi ko kuma sake naɗa shugaban ‘yan sandan, majalisar za ta cigaba da bin tsarin dokar da ake da shi na 215 da aka yi bayani a kundin tsarin mulki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *