Gwamnatin jihar Kano za ta kafa kwalejin horarwa da kuma koyar da dabarun yaki da cin hanci da rashawa a karkashin hukumar sauraren korafin Jama’a da hana rashawa ta jihar.

Tuni dai majalisar zartarwa ta jihar ta amince da kafa sabuwar kwalejin, a wani mataki na samar da kwararru kuma managartan Jami’an yaki da rashawa kamar yadda shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano Barista Muhuyi Magaji ya bayyana.

Ya ce yaran Kano za su samu horon da ya kamata su samu, kuma su kan su ma’aikata za a horar da su dabarun kauce ma cin hanci da rashawa.
Shirin dai ya na zuwa ne, a daidai lokacin da masharhanta ke ci-gaba da tsokaci game da dakatarwar da fadar shugaban kasa ta yi wa shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *