Gwamnatin Najeriya ta janye sanarwar da ta bada a baya na komawa makaranta.

Ministan Ilimi Adamu Adamu Ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan halartar taron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagotanta.

Ministan ya ce ba wata makaranta da za ta rubuta jarabawar kammala makarantar sakandire na WAEC, sabanin sanarwar da ta bayar a baya na rubuta jarabawar daga ranar 5 ga watan Augusta zuwa 5 ga watan Satumba.

Idan dai za a iya tunawa Radiyon Talaka Ya kawo muku labarin da karamin ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana cewa za a rubuta jarabawar.

Adamu ya ce ba wata makaranta da za ta bude yanzu har sai an tabbatar ba barazanar cutar korona.

Ya ce gwamnatin tarayya ta gummace dalibai su kara shekara guda da su kuma da cutar ta korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *