Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa tare da tabbatar da adalci SERAP, ta bukaci gwamnatin Nijeriya ta saki shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ibrahim Magu.

SERAP ta bayya na haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar mai taken ‘Dole a yi wa Magu adalci, ta na mai jaddada cewa ya kamata a samu Magu da wani laifin kirki tukunna.

Rahotanni sun ce kwamitin da Magu ya fuskanta ya tsare shi na tsawon sa’o’i da dama, daga bisani aka kai shi wata cibiyar binciken ‘yan sanda da ke unguwar Area 10 a Abuja ya kwana.
Sanarwar mai dauke da sa hannun mataimakin mataimakin kungiyar Kolawole Oluwadare, SERAP ta umarci hukumomi su ba Magu ‘yancin sa na fuskantar shari’a yadda ya kamata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *