Ofishin jakadanci Najeriya a kasar Kanada ya ce an kammala shirye-shiryen maido da ‘yan Najeriya da suka makale a kasar gida sakamakon barazanar cutar korona.

Ofishin jakadancin a cikin wata sanarwa ya ce kamfanin jirgin kasar Portugal na Euro Atlantic Airways ne aka zaba ya yi jigilar ‘yan Najeriyan zuwa gida.  

Sanarwar ta ce ‘yan Najeriya dake zaune a kasar dari 3 ne suka nuna sha’awarsu ta komowa gida Najeriya.

A baya an soke jirgin da aka bayyana zai fara jigilar a ranar 14 ga watan Mayu saboda sanya dokar hana sauka ko tashin jirgin sama da kasar ta Kanada ta yi.

Ofishin jakadancin ya ce kasar ta Kanada ya hana kamfanin jirgin sama  na Air Peace aikin saboda tabbatar da tsaron lafiya.

Gwamnatin Najeriya dai ta maido da ‘yan Najeriya sama da dubu 2 gida daga kasashe daban-daban tun bayan sanya dokar hana tashi ko saukar jiragen sama sakamakon bullar cutar korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *