Gwamnatin tarayya ta ce za a rubuta jarabawar kammala makarantar sakandire ta yammacin Afrika WAEC daga ranar 4 ga watan Augusta zuwa 5 ga watan Satumbar wannan shekarar.

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, ya sanar da haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron kwamitin yaki da cutar korona wanda ake shiryawa a Abuja.

Ya ce akwai shiri na musamman da za a yi ga wadanda ke so suyi bitar karatu kafin zana jarabawar.

Emeka ya ce nan gaba kadan za a sake fitar da jadawalin yanda za a rubuta jarabawar kammala makarantar sakandire na cikin gida NECO, da NABTEB.

Ya kara da cewa akwai tsare-tsare da za a yi amfani dasu wajen tabbatar da cewa dalibai da sauran ma’aikata basu shiga hadarin kamuwa da cutar ba a lokacin jarabawar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *