Za a ci gaba da rufe makarantu a Kenya har zuwa Watan Janairun 2021 sakamakon annobar cutar Corona.

Har’ ila yau an soke jarabawar zangon karatu na karshe da aka saba yi a watan Oktoba da kuma Nuwamba na kowacce shekara a kasar.

Ministan ilimi na kasar George Magoha ya ce dalibai zasu maimaita shekara daya ta karatunsu sakamakon rufe makarantun.

Sai dai za a bude jami’o’i da kwaleji a watan Satumba bisa bin dokokin masana harkar lafiya na kare kai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *