Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta fito da wasu sabbin tsare-tsare na kariya daga cutar korona a lokacin gudanar da zabubbuka.

Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu, ya kaddamar da sabbin tsare-tsaren a wajen taron kwan guda-guda da kwamitin yaki da cutar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shiryawa a Abuja.

Ihekweazu, ya ce sabbin tsare-tsaren za su taimakawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, jam’iyyun siyasa da kuma su kansu ‘yan Najeriya dake kada kuri’a a wannan lokaci na kare kai.

Shugaban hukumar ya bukaci jam’iyyun da shugabannin siyasa su yi biyayya ga sabbin dokokin domin zama abin koyi ga mabiyansu.

Sannan ya sanar da cew hukumar ta fito wani sabon shirin horaswa na musamman ta yanar gizo kan hanyoyin kariya daga cutar, wanda zai taimaka musamman ma ga ma’aikatan lafiya.  

Ya ce shirin na yanar gizo zai zama na kowa da kowa, amma  an shirya shi ne musamman kan hanyoyin da za a rage barazanar da ma’aikatan lafiya ke fuskanta na kamuwa da cutar korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *