Ministan kula da harkokin wasanni da ci gaban matasa Sunday Dare ya bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za a maido da harkokin wasanni a Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne ta bakin babban sakataren ma’aikatar Gabriel Aduda a lokacin da yake karbar takunkumin kare kai daga kamuwa da cututtuka da dalibai masu yiwa kasa hidima suka samar domin dakile yaduwar cutar korona.

A lokacin da yake yabawa hukumar ta NYSC bisa abin da suka yi, ministan ya ce ma’aikatarsa da za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an maido da harkokin wasannin ta hanyar bin matakan kariya daga cutar ta korona.

A nasa jawabin shugaban hukumar ta NYSC Shu’aibu Ibrahim, ya ce hukumar ta samar da takunkumin ne domin tabbatar da cewa an gudanar da gasar wasanni da za a gudanar a karshen wannan shekarar cikin nasara.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *