Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya ta ce an sake samun masu dauke da cutar korona 575 a jihohin 20 dake fadin kasar nan ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter, ta ce mutanen na daga cikin wadanda aka yiwa gwaje-gwajen cutar ranar Litinin a fadin kasar nan.

A cikin sanarwar, hukumar ta ce yawan masu dauke da cutar yanzu a Najeriya ya kai dubu 29 da dari 2 da 86, yayin da kuma adadin wadanda cutar ta kashe suka kai dari 6 da 54.

Haka kuma mutane dubu 11 da dari 8 da 28 sun warke daga cikin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya.

A cikin sanarwar sabbin wadanda suka kamu da cutar, jihar Lagos c eke da adadi mafiya yawa na 123 da suka sake kamuwa, sai babban birnin tarayya Abuja dake da mutane 100.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *