AHMAD LAWAN
SHUGABAN MAJALISAR DATTAWAN NAJERIYA

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce hukumar kula da harkokin da suka shafi daukar aiki ta Najeriya ke da alhakin daukar sabbin ma’aikata dubu dari 7 da 74 a kananan hukumomin Najeriya.

Lawan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce ya zama wajibi hukumar da ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi su yi cikakken bayani kan hanyoyin da suke so su bi wajen daukar ma’aikatan.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan majhalisar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da shirin biyo bayan sabani da aka samu tsakanin kwamitin da ta kafa da karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi Festus Kayemo.

A ranar Talatar da ta gabata ne kwamitin majalisar ya kori ministan sakamakon kin bada hakuri da ya yi kan zargin daga musu murya a lokacin da yake jawabi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *