Hukumar jami’an tsaron farin kaya Civil Defence ta ce ta kwato basussukan da suka kai naira milliyan 9 da dubu dari 7 a jihar Jigawa cikin watanni 6 da suka gabata.

Mai magana da yawun hukumar Adamu Abdullahi, ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar.

Abdullahi ya ce hukumar ta karbo hudaden ne sakamakon koke-koken da ta yi ta samu daga hukumomin da suka tura kudaden ga wadanda suka karbi basussukan.

Ya ce kwato kudaden na daga cikin manyan ayyuka dari da 14 da hukumar ta maida hankali akai daga watan Janairun wannan shekarar zuwa Yuni.

Ya ce basussuka da sauran aikace-aikacen da suka shafi hakan sun ragu idan aka kwatanta da irin bayanan ayyuka da hukumar ta samu a baya.

A cikin sanarwar shugaban hukumar a jihar Garba Muhammad ya bukaci al’ummomi su ci gaba da rungumar zaman lafiya da kaucewa duk wasu rigingimu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *