Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta kubutar da rayukan mutane dari 4 da 30, da kudi naira billiyan 3 a gobara dari 4 da 96 da ta kai dauki cikin watanni 6.

Mai magana da yawun hukumar Saidu Mohammed ya sanar da haka a Kano.

Mohammed y ace mutane 74 ne suka rasa rayukansu, tare da asarar naira milliyan dari 5 da 34, a tsakan kanin watannin Janairu zuwa Yunin wannan shekarar.

Ya ce hukumar ta samu kiraye-kirayen kai dauki sau dari 2 da 60, wanda daga cikin su guda 100 an kira ne inda aka bada rahoton gobara na karya.

Hukumar mafiya yawan gobarar na tashi ne sanadiyyar hadurran mota, amfani da kayayyakin girki dake amfani da wutar lantarki, da kuma iskar gas.

Hukumar ta bukaci al’umma da su yi taka-tsantsan da yadda suke amfani da wuta, tare da sanya ido akan ‘ya’yansu a koda yaushe.  

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *