Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta karyata rade-radin da ake yadawa a kafofin sadarwa na kama shugaban ta Ibrahim Magu.

Mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale, ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a Abuja.

Oyewale, ya ce Magu ya amsa gayyata ne da kwamitin da aka kafa ya masa zuwa fadar shugaban kasa.

Ya kara da cewa an mikawa shugaban hukumar EFCCn ne a lokacin da yake hanyar zuwa shelkwatar hukumar dake Abuja, domin halartar taro.

Sanarwar na zuwa ne jim kadan bayan hukumar jami’an tsaron farin kaya DSS ta karyata cewa ta kama shugaban hukumar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *