LAI MOHAMMED
MINISTAN YADA LABARAI

Gwamnatin tarayya ta sanar da yi wa gidajen rediyo da talabijin rangwamin kashi 60 cikin 100 na basukan da ta ke binsu.

Cikin wata sanarwa, ministan yada labaraI Lai Muhammad ya ce gwamnati ta dauki matakin ne don rage musu radadin rashin kudaden shiga saboda annobar cutar korona.

Mohammed ya ce gwamnatin na bin wasu kafafen yada labarai na rediyo da talabijin bashin kudade da ya kai naira biliyan bakwai da miliyan dari takwas.

Ya ce duk wadanda ake bi bashin su hanzarta biyan kashi arba’in cikin dari na abin da ake binsu cikin watanni uku masu zuwa.

Sanarwar ta kara da cewa ana bin gidajen rediyo da dama basussuka mai yawa lamarin da ya sa wasu ma ke fuskantar barazanar kin sabunta musu lasisi.

Shugabar Kungiyar kafafen watsa labarai na rediyo da talbijin a Najeriya kuma shugabar gidan talabijin na Abubakar Rimi a Kano Sa’a Ibrahim, ta ce sun yi farin ciki da wannan matakin.

Tun da farko dai kungiyar ce ta nemi gwamnatin tarayya ta sassauta mata basussukan, saboda annobar korona ta durkusar da harkokin tallace-tallace a kafafen.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *