Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan yadda ake samun yawaitar sabbin masu kamuwa da cutar korona  musamman a tsakanin manyan jami’an gwamnati.

Shugaban kwamitin yaki da cutar a Najeriya Boss Mustapha, ya sanar da haka a wajen taron da kwamitin ke shiryawa kullum a Abuja.

Mustapha wanda shine sakaren gwamnatin tarayya, ya ce hakan na da matukar hadari ga Najeriya da kuma harkokin gudanar da mulki.

Ya ce duk da cewa an shiga mataki na gaba na sassauta dokar takaita zirga-zirga domin dakile yaduwar cutar, akwai bukatar ‘yan Najeriya su ci gaba da daukar matakan kariya da muhimmanci.

Mustapha ya kara da cewa bisa la’akari da yadda ake samun karuwar sabbin masu dauke da cutar a duniya da cikin gida Najeriya, ya kamata a san cewa ba a yaki cutar ba.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba matakan yaki da cutar da muhimmanci, tare da yin dukkanin abubuwan da suka kamata. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *