Fadar shugaban kasa ta dakatar da shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC Ibrahim Magu.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar da haka ga manema labarai a ranar a Abuja.

A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na almundahana.

A ranar ta Litinin ne hukumar jami’an tsaron farin kaya DSS da kuma EFCC suka bayyana cewa ba kama Magu akayi ba.

EFCC ta ce ya amsa gayyatar jami’an tsaro ne kawai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Aslm lna goyan bayan Gwannatin jihar kaduna da sasanya dokan hana beli gaduk wanda aka kamashi da laifin feyde.Allah ya’lda nufi.sako daga Abubakar M Ya’u mai waka kaduna.