Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta kashe naira milliyan 30 a shirin yiwa ‘yan ta’adda da barayin shanu da suka tuba a sassan jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa, ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.

Ya ce an kashe akasarin kudaden ne wajen sayen makaman dake hannun tubabbun ‘yan ta’addan, a yunkurin karbe dukkanin makaman da suka mallaka.

Inuwa ya ce an maida wasu kudade da ba a kashe ba, zuwa asusun gwamnatin jihar a lokuta da dama.

Gwamnatin jihar dai ta fito da shirin yin afuwar ne ga ‘yan ta’addan da barayin shanu domin tabbatar da zaman lafiya da yaki da ayyukan ta’addanci a jihar.

Sai dai a watan da ya gabata gwamnan jihar Aminu Bello Masari, ya sanar da soke shirin sakamakon rashin tasiri ga hare-haren da ake kaiwa a jihar.

Masari ya ce gwamnatin jihar ba za ta sake yin wata tattaunawar sulhu da ‘yan ta’addan ba kamar yadda ta bada gargadi a baya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *