Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya ce bangaren shari’a na jihar ba zai sake bada belin duk wanda aka kama da laifin aikata fyade a fadin jihar ba.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a lokacin da hadakar kungiyoyin mata suka yi tattaki na musamman zuwa gidan gwamnatin jihar domin neman a biwa wadanda aka yiwa fyade hakkinsu.

Ya ce shugaban alkalan jihar ya bada tabbacin cewa daga yanzu ba za a sake bada belin wanda aka samu da aikata laifin ba, saboda suna sake aikata laifin bayan an sake su.

A cewarsa majalisar dokokin jihar ta fito da doka ta musamman da za ta bada damar hukunci mai tsauri ga duk wanda aka kama da laifin fyade a fadin jihar.

El-Rufai, ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar daukar matakin cirewa duk wanda aka samu da laifin mazakuta ta hanyar yi masa aiki na musamman.

A cewarsa wani dan majalisar dokokin jihar ya gabatar da kudurin dandake duk wanda aka kama ga majalisar dokokin jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *