‘Yan ta’ adda sun kashe mutane 15 a wani hari da suka kai kauyen ‘Yar Gamji, dake karamar hukumar Batsari. 

A lokacin da yake tabbatar da kai harin hakim in Batsari Tukur Mu’azu, ya ce ‘yan ta’ addan da suka shiga kauyen akan babura sun kashe mutanen ne a gonakin su. 

Ya ce baya ga wadanda aka kashe akwai mutane biyar da ba a san inda suka shiga ba. 

Ya ce an aje gawarwakin ne a Babban Asibitin Garin Batsari, Kuma gobe za a yi jana’izarsu, sannan akwai mutane 2 da ‘yan ta’ addan suka raunata, suma suna asibitin. 

Shima mai magana da yawun rundunar’yan sandan jihar, SP Gambo Isa ya tabbatar da kai  harin, inda ya ce rundunar ta tura jami’an ta a yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *