Rundunar sojin Nijeriya, ta ce dakarun ta sun kashe mayakan Boko Haram 75 a cikin watan Yunin da ya gabata a yankin arewa maso gabas.

A cikin wata Sanarwa da ta fitar, ma’aikatar tsaro ta ce dakarun Nijeriya sun yi arangama har sau 17 da mayakan Boko Haram a cikin watan Yuni, inda su ka kwace wasu motoci da makamai da dama daga mayakan.

Sanarwar ta cigaba da cewa, dakarun sun kuma yi nasarar ceto fararen hula 35 da mayakan kungiyar su ka yi garkuwa da su, yayin da su ka kama mayakan hudu ciki har da matan kwamnadan kungiyar na shiyyar Adamawa da aka bayyana sunayen su da Aishatu Manye da Kelune Mate, da wani dan leken asirin kungiyar mai suna Kawalu.

A baya-bayan nan dai, ana ci-gaba da yin kare jini biri jini tsakanin Sojojin da mayakan Boko Haram, bayan Janar Tukur Burutai ya sha alwashin kammala kakkabe mayakan kungiyar ta’addancin cikin sauri.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *