Jam’iyyar PDP ta bayyana kiran da jam’iyyar APC ta yi cewa a tuhumi wasu manyan PDP da ta ce su na da alaka da dan damfara Hushpuppi a matsayin abin da bai dace ba.

PDP ta ce hakan ya nuna irin bakar aniyar da ‘yan APC ke fama da ita, baya ga mugun nufin bi-ta-da-kulli a kan ‘yan adawa.

A cikin wata sanarwa da Kakakin jam’iyyar PDP na Kasa Kola Olagbondiyan ya fitar, ya ce wannan mummunan zargi da APC ta yi, ya nuna yadda ta ke kitsa karya da sharri da tuggu a kan masu adawar da ba su ji ba, ba su gani ba.

Daga cikin wadanda APC ta bukaci a tuhuma dai akwai Atiku Abubakar da Bukola Saraki da Yakubu Dogara da kuma Dino Melaye.

Jami’an tsaro sun kama Hushpuppi da aka sani da Raymond Abbas a Dubai, daga nan aka aika shi Amurka a hannun jami’an FBI.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *