Kwamitin binciken wasu zarge-zarge da ake dangantawa da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gayyaci shugaban hukumar Ibrahim Magu.

An tsaida Magu ne a lokacin da yake barin ofishin hukumar ta EFCC dake Wuse II, inda aka mika masa takardar gayyatar tare da tabbatar masa cewa kwamitin na jiransa a fadar shugaban kasa.

Magu a lokacin ya bayyanawa wadanda suka kawo masa takardar gayyatar cewa zai fara zuwa shelkwatar hukumar, inda nan take suka maida masa martani cewa zuwansa gaban kwamitin ya fi muhimmanci akan aikin da zai gudanar a shelkwatar hukumar.

Tuni dai lauyansa Rotimi Jocob, ya isa inda ake tattaunawar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *