Gwamnatin Tarayya ta ce an bi dukkan ka’idoji da sharuddan da doka ta tanada wajen dakatar da Shugaban Hukumar Zuba Jarin Inshorar Ma’aikata da wasu daraktocin hukumar.

Bayanin ya fito ne, bayan wani bangare na Kungiyar Kwadago ya zargi gwamnati cewa ba ta bi ka’idojin da su ka dace ba wajen dakatar da manyan mahukuntan hukumar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar, Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Kwadago Charles Akpan, ya ce tabbas gwamnati ta bi duk wata hanyar da ta dace sannan ta dakatar da su.

Akpan ya ce daga cikin dalilan dakatar da mutanen akwai yadda su ka wawure naira biliyan 3 da miliyan 400, aka rika kirkiro kwangilar cuwa-cuwa domin a rika karkatar da kudaden.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *