Tsohon gwamnan jihar Kaduna Abdul-Kadir Balarabe Musa, ya ce sabuwar kungiyar siyasa ta National Consultative Forum a turance za ta shawo kan matsalar shugabanci nagari a Nijeriya.

Balarabe Musa ya kara da cewa, ya amince da sabuwar kungiyar domin ceto Nijeriya daga matsanantan matsalolin da ta ke fuskanta.

Kungiyar dai ta sanar da kafuwar ta ne ta bakin tsohon gwamnan a karkashin mulkin soji Abubakar Umar.

Balarabe Musa tare da sauran ‘yan kungiyar sun sanar da cewa, ba a yi wa Nijeriya mulkin da ya dace kuma hakan ne ya sa ta ke bukatar ingantaccen shugabanci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *